Matthew 12

Ubangijin Asabbaci

1A lokacin nan Yesu ya bi ta gonakin hatsi a ranar Asabbaci. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara kakkarya kan hatsi suna ci. 2Saʼad da Farisiyawa suka ga wannan, sai suka ce masa, “Duba! Almajiranka suna yin abin da doka ta hana a yi a ranar Asabbaci.”

3Sai ya amsa, ya ce, “Ba ku karanta abin da Dawuda ya yi ba ne saʼad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa? 4Ya shiga gidan Allah, da shi da abokan tafiyarsa suka ci keɓaɓɓen burodin-wanda doka ta hana su yi, sai firistoci kaɗai. 5Ko kuwa ba ku karanta a Doka cewa a ranar Asabbaci firistoci sukan karya dokar Asabbaci duk da haka ba da yin wani laifi ba? 6Ina faɗa muku cewa wani
Ko kuwa wani abu; haka ma a ayoyi 41 da 42
wanda ya fi haikali yana a nan.
7Da a ce kun san abin da waɗannan kalmomi suke nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,’
Hos 6.6
da ba ku zargi marar laifi ba.
8Gama Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabbaci.”

9Da ya ci gaba daga wurin, sai ya shiga majamiʼarsu, 10a nan kuwa akwai wani mutum mai shanyayyen hannu. Don neman dalili su zargi Yesu, sai suka tambaye shi suka ce, “Ya dace a warkar a ranar Asabbaci?”

11Ya ce musu, “In waninku yana da tunkiya, ta kuma fāɗa a rami ran Asabbaci, ba zai cire ta daga ramin ba? 12Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja! Saboda haka ya dace a yi alheri ran Asabbaci.”

13Saʼan nan ya ce wa mutumin, “Miƙa hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye, kamar dai ɗayan. 14Amma Farisiyawa suka fita suka ƙulla shawara yadda za su kashe Yesu.

Zaɓaɓɓen Bawan Allah

15Da ya gane wannan, sai Yesu ya janye daga wurin. Da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da dukan masu ciwonsu, 16yana jan musu kunne kada su faɗa wa kowa akan ko shi wane ne. 17Wannan kuwa domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya ne cewa:

18“Ga bawana da na zaɓa,
ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi;
zan sa Ruhuna a kansa,
zai kuma yi shelar adalci ga alʼummai.
19Ba zai yi faɗa ko yǎ ɗaga murya ba,
ba kuwa wanda zai ji muryarsa a kan tituna.
20Kyauron da ya tanƙwasa ba zai karye shi ba.
fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba,
sai ya jagoranci adalci zuwa ga nasara.
21Cikin sunansa alʼummai za su dogara.”
Ish 42.1-4

Yesu da Beʼelzebub

22Sai aka kawo masa wani bebe kuma makaho mai aljani, Yesu kuwa ya warkar da shi, har ya iya magana ya kuma sami ganin gari. 23Dukan mutane suka yi mamaki, suka ce, “Wannan Ɗan Dawuda ne kuwa?”

24Amma da Farisiyawa suka ji haka, sai suka ce, “Ahab, da Beʼelzebub
da Girik Beʼezeboul ko kuwa Beʼelzeboul; haka ma a aya 27
sarkin aljanu ne kaɗai, wannan mutum yake fitar da aljanu.”

25Yesu kuwa ya san tunaninsu sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa zai lalace, kuma duk birni ko gidan da yake rabe gāba da kansa ba zai ɗore ba. 26In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, ai, ya rabu yana gāba da kansa ke nan. Yaya kuwa mulkinsa zai ɗore? 27In kuwa ta wurin Beʼelzebub nake fitar da aljanu, to, ta wa mutanenku suke fitar da su? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku. 28Amma in ina fitar da aljanu ta wurin Ruhun Allah ne, to, fa, mulkin Allah ya zo muku ke nan.

29“Ko kuwa, yaya wani zai iya shiga gidan mai ƙarfi yǎ ƙwace masa kaya ba tare da ya fara ɗaure mai ƙarfin nan tukuna ba? Saʼan nan zai iya washe gidansa.

30“Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni ne, kuma wanda ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi. 31Saboda haka ina gaya muku, za a gafarta wa mutane kowane zunubi da kuma saɓo, amma saɓo game da Ruhu, ba za a gafarta ba. 32Duk wanda ya zargi Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya zargi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, ko a wannan zamani ko a zamani mai zuwa.

33“Itace mai kyau, yakan ba da ʼyaʼya masu kyau. Itace marar kyau kuma, yakan ba da ʼyaʼya marasa kyau. Itace dai, da irin ʼyaʼyansa ne ake gane shi. 34Ku macizai, ta yaya ku da kuke mugaye za ku iya magana kirki? Gama daga baki, mutum yakan faɗi abin da yake cikin zuciya. 35Mutumin kirki yakan fito da abubuwa masu kyau daga ajiyar da aka a yi cikinsa, mugun mutum kuwa yakan fito da mugayen abubuwa daga cikin muguntar da aka yi ajiya a cikinsa. 36Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shariʼa a kan kowace kalmar banza da suka faɗa. 37Gama ta wurin kalmominka za a kuɓutar da kai, kuma ta wurin kalmominka za a hukunta ka.”

Alamar Yunana

38Saʼan nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka ce masa, “Malam, muna so mu ga wata alama mai banmamaki daga gare ka.”

39Sai ya amsa, ya ce, “Mugu da mazinacin zamani yana neman wata alama mai banmamaki! Amma babu wadda za a nuna musu, sai dai alama ta annabi Yunana. 40Gama kamar yadda Yunana ya yi yini uku da kuma dare uku a cikin wani babban kifi, haka Ɗan Mutum zai yi yini uku da kuma dare uku a cikin ƙasa. 41Mutanen Ninebe za su tashi a ranar shariʼa tare da wannan zamani, su kuwa hukunta shi; don sun tuba saboda waʼazin Yunana, yanzu kuwa ga wanda ya fi Yunana girma a nan. 42Sarauniyar Sheba za ta tashi a ranar shariʼa tare da wannan zamani, ta kuwa hukunta shi; don ta zo daga ƙarshen duniya, ta saurari hikimar Solomon, yanzu kuwa ga wanda ya fi Solomon girma a nan.

43“Saʼad da mugun ruhu ya fita daga mutum, yakan bi wuraren da ba ruwa yana neman hutu, ba ya kuwa samu. 44Saʼan nan yakan ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’ Saʼad da ya iso, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, kuma a kintse. 45Sai yǎ je yǎ ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, su kuwa zo su shiga su zauna a can. Ƙarshen mutumin nan fa zai fi farkonsa muni. Haka zai zama ga wannan mugun zamani.”

Mahaifiyar Yesu da ʼYanʼuwansa

46Yayinda Yesu yake cikin magana da taron, sai ga mahaifiyarsa da ʼyanʼuwansa tsaye a waje, suna so su yi magana da shi. 47Wani ya ce masa, “Mahaifiyarka da ʼyanʼuwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai.”
Waɗansu rubuce rubucen hannu na dā ba su da aya 47.


48Ya amsa masa ya ce, “Wace ce mahaifiyata, su wane ne kuma ʼyanʼuwana?” 49Sai ya miƙa hannu wajen almajiransa, ya ce, “Ga mahaifiyata da kuma ʼyanʼuwana. 50Ai, duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda yake cikin sama, shi ne ɗanʼuwana da ʼyarʼuwata da kuma mahaifiyata.”

Copyright information for HauSRK